Ba mu yarda da yunkurin kwace mana filin Husainiyya Bakiyyatullah Zariya ba

Ba mu yarda da yunkurin kwace mana filin Husainiyya Bakiyyatullah Zariya ba*

A ranar 20/07/17 ne aka ga wasu sojojin rundunar sojin Nijeriya suna ba da kariya ga wasu leburori da gwamnati ta yi hayar su don katange filinmu, inda Cibiyar Musulunci ta Husainiyya Bakiyattullah take, kafin rusa ta da sojoji suka yi yayin da suka kawo harinsu na kisan kiyashi a Disamban 2015.

Hukumar kula da ci gaban birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) da jami’anta sun nuna rashin masaniyarsu dangane da wannan gini da ake yi a filinmu yayin da aka tuntube su. Wannan shi ya kara tabbatar da zargin da ake yi cewa, wannan aiki ne na gwamnatin Tarayya karkashin kulawar sojoji kai tsaye, wadanda suke da boyayyar bukata na kwace filin tun da dadewa.

Muna so mu jawo hankulan jama’a da kuma al’ummar kasa da kasa zuwa ga cewa, wannan fili da aka gina Husainiyya Bakiyyatullah a kansa, an mallake shi ne daga wadanda suka mallaki filin tun asali. Muna da dukkan takardun da suka dace kan haka. Kuma duk da cewa, an rurrusa ta ba tare da hujja ta shari’a ba daga hadin gambizar sojoji da gwamnatin jihar Kaduna karkashin Elrufa’i, filin dai namu ne. Don haka gwamnatin Tarayya ba ta da wata hujja na yin gini a filin da ba nata ba. A hakikanin gaskiya wannan shi ne share-wuri-zauna mafi muni.

Kuma yana da kyau a lura cewa, rusa Husainiyya yana cikin wuraren da yanzu haka an shigar da kara a kansa a gaban kotun Tarayya da ke Kaduna. Har ila yau kuma, wannan wuri, wuri ne da aka aikata laifi a kansa, inda gwamnati ta kashe daruruwan fararen hula ‘yan kasa. Don haka kuskure ne babba gwamnati da rana tsaka ta ce za ta lalata shaidar ta’annutin da aka yi a wurin.

A sarari yake cewa, wannan yunkuri na baya-bayan nan na kwace mana fili wani ci gaba ne na danne mana hakkinmu na ’yan Adam. Mun yi amanna cewa, wannan yunkuri na katange filinmu wani yunkuri ne na kara boye irin ta’addancin da sojoji suka yi a kisan kiyashin Disamban 2015.

Haka nan kuma lokacin da aka zaba don yin wannan ginin ya ba masu nazarin al’amuran yau da kullum mamaki, saboda an yi shi ne a lokacin da aka labarto cewa gwamnatin Tarayya na neman wasu hanyoyin lalama don warware matsaloli da rashin tabbas din da ci gaba da tsare Jagoranmu Shaikh Zakzaky yake jawowa a duk fadin duniya. Da alama kurayen da ke cikin gwamnatin nan suna yin wani sabon yunkuri don wargaza neman sulhun da ita gwamnatin ke yi kan kisan kiyashin Zariya da sojojinta suka yi. To, muna so mu tunatar da wadannan kurayen cewa, kamar yadda kudurin doka na Rome da suka kafa kotun manyan laifuka na ICC suka nuna, rusa wuraren ibadu kamar Husaniyya Bakiyyatullah ta Zariya yana daga cikin manyan laifukan yaki.

Muna so a sani a sarari cewa, mu ba za a tunzura mu ba ta kowace hanya. Za mu ci gaba da neman hakkokinmu da tsarin mulki ma ya tabbatar mana da su ta hanyar shari’a da kuma muzaharori na lumana, kamar yadda aka san mu da shi tun shekaru da dama da suka shude. Don haka muna kara jaddada bukatarmu na a saki Shugabanmu, Shaikh Zakzaky da matarsa da sauran ’yan uwa da suke tsare da gaggawa, kuma nan take.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA IMN
Skype: Ibrahim.musa42
22/07/17

Image may contain: cloud, sky, outdoor and nature
Image may contain: cloud, sky, outdoor and nature
Image may contain: sky, cloud, tree, outdoor and nature

Shugaban Izala ya koko

Bala lau ya koka da yadda ake samun karuwar masu kallon tashan Al-wilaya Tv da yadda aka dena kallon sunna tv. Yayi wannan korafin ne lokacin da ya kaiwa sarkin Doma Alh. Aliyu Ogah gaisuwa a fadarsa dake cikin garin Doma, Jihar Nasarawa. Inda yake cewa su sun bude. Sunna Tv da jama’a na kallon su amma an dena an koma kallon Al-wilaya Tv, meye jama’a suke nufi suna son a yada shi’a kenan? Meye ra’ayin ku jama’a akan wannan korafi nasa?

JAMILA NAGUDU TA GODEWA MASOYANTA

JAMILA NAGUDU TA GODEWA MASOYANTA

Fitacciyar jarumar kannywood jamila nagudu ta godewa ‘yan uwa da abokan arziki wa’yanda suka duba ta da kuma yi mata addu’a lokacin da ta kwanta rashin lafiya.
A wani sakon da ta wallafa a shafin ta na instagram, jarumar ta ce “Allah mungode maka,Allah ka kara mana lafiya.Marasa lafiya na gida da asibiti.

Image may contain: 1 person, smiling

JAMHURIYAR MUSULUMCI TA IRAN AYAU

JAMHURIYAR MUSULUMCI TA IRAN AYAU.
_____

IRAN TAKAI MASTAYIN DOGARO DAKAI AGUN KERA MAKAMAI MASU LINZAMI DA BAMABAMAI.

Kwamandan Dakarun kare sararin samaniyya na dakarun kare juyin juya Halin Musulunci na kasar Iran, Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh ya bayyana cewar ; Ahalin yanzu Iran ta
kai matsayin dogaro da kanta a fagen samar da makamai masu linzami, jirage marasa matuka da kuma bama-bamai.

Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh ya
bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi a jiya Talata da wasu daga cikin ‘yan majalisar shawarar Musulunci ta kasar ta
Iran.

Inda ya ce kaiwa matakin dogaro da kai wajen kera makamai masu linzami na zamani, jirage marasa matuka, bama bamai, da Na’urorin rada-rada na kariya
da gano makaman makiya bugu da kari kan Na’urori na sadarwa na yaki, lamari ne
da ke nuni da Iran tana iya magance dukkanin matsalolin da take fuskanta
ta hanyar dogaro da irin karfi na cikin gida da take da shi.

Yayin da yake magana kan harin da dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka kai wa ‘yan ta’addan Da’esh A garin Deir Zur na kasar Siriya da makamai masu linzami kuwa a kwanakin baya.

Janar Hajizadeh ya ce makamai masu linzamin sun tarwatsa sansanonin cikin
kasa na ‘yan ta’addan gaba daya da ke wajen, yana mai sake jaddada aniyar dakarun Nasu na mayar da martani ga duk wata barazana da kasar Iran za ta iya fuskanta daga makiya.

A ranar 18 ga watan Yunin dakarun kare juyin juya halin Musuluncin suka kai hari da makamai masu linzami guda shida ga
sansanin ‘yan ta’addan Da’esh din a garin na Deir Zur da ke kasar Siriya inda suka sami nasarar hallaka ‘yan ta’adda sama da 170 , cikinsu kuwa har da wasu manyan kwamandojinsu su 6.

Harin dai ya biyo bayan harin ta’addanci ne da ‘yan Da’esh din suka kai haramin marigayi Imam Khumaini (r.a) da kuma wani bangare na majalisar shawarar Musulunci ta kasar Iran a ranar 7 ga watan Yunin.
_______________

Image may contain: 2 people
Image may contain: 2 people, indoor

TAKARDAR MANEMA LABARAI

TAKARDAR MANEMA LABARAI

El-Zakzaky

An bankado wani sabon makirci na yunkurin halaka Shaikh Zakzaky da kuma dirar wa ‘yan uwa na Harkar Musulunci*

Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) na son janyo hankalin al’umma dangane da wani makirci da makiya son zaman lafiya suka shirya a Najeriya. Wannan sabon makirci, kamar yadda majiya mai inganci ta tabbatar mana, ya kunshi halaka Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda a halin yanzu yake tsare ba bisa doka ba, wanda kin bin umurnin kotu na sakin sa ne, tare da kuma auka wa ‘yan uwa Musulmi a garuruwa da dama na arewacin kasar nan a lokaci guda.

Kamar yadda suka tsara, za a fara ta’addancin a kan IMN ne da zarar an yi wata ‘muhimmiyar sanarwa mai matukar amfani’ a kwanaki kadan masu zuwa ko kuma makonni. Wadanda suka shirya makircin na son yin amfani da yanayin rashin tabbas da sanarwar za ta haifar a siyasance wanda zai ba su damar karasa mummunar manufarsu na kisan kiyashi da suka yi kuduri shekaru da dama, wanda ya bayyana karara a harin ta’addanci na shekarar 2015. Ta hanyar aikata mummunan kudirin nasu na kashe Jagoranmu da kuma shekar da jinainen ‘yan kasa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, suna da burin kawo karshen Harkar Musulunci har abada.

Muna sane kuma da cewa tuni an jibge gungu-gungu na jami’an tsaro cikin sirri a manyan garuruwan da za a gudanar da harin; suna jiran ranar da za a yi ‘sanarwar ta musamman’, wanda zai su damar kashe bayin Allah wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Za mu so mu yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su tursusa gwamnatin Tarayya ta tsawatar wa jami’an tsaron ta, wanda kamar har yanzu ba su gamsu ba da rayuka fiye da dubu da suka kashe a Zariya a watan Disambar 2015.

Kashe Jagoranmu Shaikh Zakzaky da kuma ‘yan uwa na IMN, ba zai amfanar da Najeriya da kuma ‘yan kasa da komai ba! Saboda haka muna kira gare su (yan kasa) da su gaggauta dakatar da wannan shirin kisa da aka shirya.

Za mu ci gaba da neman tabbatar da adalci ga wadanda harin ta’addancin sojojin Najeriya na kisan kiyashin Zaria ya shafa ta hanyoyin lumana kamar yadda muka saba. Saboda haka ne ma muke kara jaddada bukatar mu na a gaggauta sakin Jagoranmu Shaikh Ibraheem Zakzaky kamar yadda babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da umurni.

Mutane masu fata na gari, ba wai a Najeriya kawai ba, a fadin duniya baki daya, na nuna damuwa matuka dangane da makomar Shaikh Zakzaky, wanda yake gaf da cika kwanaki 600 cif bisa tsarewar zalunci. Muna son a sake shi yanzu, tare da Mai dakinsa da dukkan ‘yan uwan da ke tsare tun bayan kisan kiyashin Zariya.

Sa Hannu:
IBRAHIM MUSA
Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci a Najeriya
Skype: Ibrahim.musa42
19/07/2017

Gwamnoni nijeriya suna karbi sama da N243 BILIYON

Gwamnatin tarayya ta baiwa Gwamnoni kudin Paris club kimanin naira biliyon 243. kowani Jihar ga abinda yasamu

Abia N5.715,765,871.48b

Adamawa N6.114,300,352.68b

Akwa-Ibom N10,000,000,000b

Anambara N6.121,656,702,34b

Bauchi 6.877,776,561,25b

Bayelsa N10,000,000,000b

Benue N6.854,671749,25b

Borno N7.340,934,865,32b

Cross River N6.075,343,946,93b

Delta N10,000,000,000b

Ebonyi N4.508,083,379,98b

Edo N6,061,126,592,49b

Ekiti N4.772,836,647,08b

Enugu N5.361,789,409,66b

Gombe N4.472,877,698,19b

Imo N7.000,805,182.97b

Jigawa N7.107,666,796,76b

Kaduna N7.721,729,227,55b

Kano N10,000,000,000b

Katsina N8.202,130,909,85b

Kebbi N5.977,499,491,45b

Kogi N6,027,727,595,8b

Kwara N5,120,644,326,57b

Lagos N8.371,938,133,11b

Nasarawa N4.551,049,171,12b

Niger N7.210,793,154,95b

Ogun N5.739,374,694,46b

Ondo N7,003,648,314,28b

Osun N6.314,106,340,62b

Oyo N7.901,609,864,25b

Plateau N5.644,079,055,41b

Rivers N10,000,000,000,b

Sokoto N6.441,128,546,76b

Taraba N5.612,014,491,52b

Yobe N5.413,103,116,59b

Zamfara N5.442,385,594,49b

Abuja N685,867,500,04m

jimlar kudin ya kama N243,795,465,195,2

wannan shine karo na biyu da gwamnatin tarayya take baiwa Gwamnoni irin wannan kudin saboda ayyukan cigaba kamar abubuwan da suka dame alumman kasa gina hanyoyi biranai da karkara da samar da kanana Asibitochin . da batun biyan albashi amma haryanzu kasan nan bata warware daga wadannan matsalolin MFNS8iQ4ba